
A shafinmu kawai
A ranar Lahadi 4 ga watan Yulin da muke ciki ne, aka Kammala bitar harshen Larabci wadda ofishin JKMD a Sinigal ya shirya wa malumman Larabci a Tiyas. Bitar ta samu halartar malumma 50 maza da mata inda aka ba su laccoci kan hanyar karantar da Larabci a kwana hudu jere.
Wagga bitar tana zuwa ne cikin jerin ayyukan hadin guiwa tsakanin JKMD da ma'aikatar ilimi a Sinigal ta bangaren ilimi. Bikin bude ayyukan bitar ya samu halartar manyan ma'iakata, da maneman labarai da dama.
A nasu jawabi, mahalartan sun jinjina wa JKMD bisa hidimomin da take yi wa Muslunci da Musulmai a ko'ina a duniya musamman a Sinigal; sannan sun yi kira ga hukumar Sinigal da ta kara kula da karatun Larabci a kasar.