Mashiga

Ayyukan da’awa

Kasidar sati

A cikin shekara ta goma bayan aiko annabi Muhammad (SAW) wadda aka kira wannan shekarar da shekarar bakin ciki, saboda rasuwar Abu dalib, da kuma uwar muninai nana Khadija bint Khuwailid, da kuma dawowarsa daga Da'ifa, bayan ya hadu da waita iri-iri, da kuma munanan halaye da mutan Da'ifa suka nuna masa, sai Allah (SWT) Ya girmama annabinSa ta inda yayi Isra'i da shi, malamin tarihi dan Sa'ad ya fada cewe : Annabi (SAW) ya kasance yana zuwa matatarar
المزيد

Rahoton wata-wata

Allah Madaukakin sarki Shi ne ya bawa bayinSa mutane da aljanu ni`imar hankali don rahamarSa garesu, don haka suka zamo masu lura da tantance baki da fari, sun san me ya kamata a tunani da hankali, kuma sun san akasin hakan. A dalilin wannan ni`ma ce ta hankali da Allah Ya yi wa wadannan bayi naSa a doron kasa,
المزيد

Who's Online Now

Until today


Browsing Now (4) Visitor:
America America (3)
Mexico Mexico (1)
31/12/2008
Jawabin JAMUD dangane da kisan kiyashi da Yahudawa ke yi wa Musulmi a Zirin Gaza
Tun a karshen shekara aka fara farfagandar gudanar da wannan kisan kiyashi ta hanyar yi wa Palasdinawa Alkawuran karya da dama, da yaudarar tattauna fahimtar juna, wanda manufarta shi ne yarda da kasar Yahudawa 'yan kama wuri zauna, wanda sakamakonta irin wannan kisan kiyashi ya kasance a zirin Gaza, wanda ya dauki salon kan mai uwa da wabi, inda aka rasa rayukan daruruwan yara da tsofi da mata, wasu kuma suka yi rauni, kuma hakan na faruwa ne akan idon duniya,
31/12/2008
JKMD ta shirya bitar Alkur’ani a Gambiya
Cikin jerin ayyukan da JKMD ke yi na kula da Alkur’ani mai girma ofishinta dake Gambiya ya shirya bitar Alkur’ani a kasar karkashin taken “ Ta ya za mu karanta Alkur’ani” bitar da kwararrun alarammomi ke kula da ita ta samu halartar dalibai 50 daga makarantun islamiyya shauku dake sassan Gambiya da dama
31/12/2008
Kwalejin da’awa ta ba wa Abdallah Jaikete shaidar kammala digiri na 2
A ranar Laraba 24 ga watan Disamaba da muke ciki kwalejin da’awa ta yaye daya daga ciki dalibanta na bangaren karatu mai zurfi mai suna Abdallah Ahmad Jaikete wanda ya fito daga jamuhuriyyar Mali, inda aka gudanar da tattauna bincike da ya gabatar karkashin taken “Gudummawar Shekh Sidi Muhktar Konta na adabi a yammacin Afurka” wanda aka gudanar a dakin taro na dakta Ahmad Khalifi karkashin kulawar dakta Hashim Mahdi Shirif.
31/12/2008
Kwalejin da’awa ta yaye Ibrahim Musa daga Itofiya
A ranar Lahdi 28 ga watan Disamaba da muke ciki kwalejin da’awa ta yaye daya daga ciki dalibanta na bangaren karatu mai zurfi mai suna Ibrahim Musa Balla wanda ya fito daga Itofiya, inda aka gudanar da tattauna bincike da ya gabatar karkashin taken “Da’awar Musulunci tsakanin farkawar Musulunci da
30/12/2008
JKMD ta halarci baje koli a kasar Mali
JKMD ta halarci baje koli na kungiyar tattalin arziki ta kasashen yammacin Afurka da aka gudanar a kasar Mali daga ranakun 20 har zuwa 30 ga watan Disamba, inda rumfar JKMD ta tattara wasu Alkur’anai masu falle daban-daban, da tarjamomin ma’anar Alkur’ani, da kuma wasu littattafai na wayewa, tare da hotuna dake nuna ayyukan da JKMD ke gudanarwa a bangarori daban-daban,
29/12/2008
JKMD ta halarci taron kara wa juna sani a Potugal
JKMD ta halarci taron kara wa juna sani a Potugal, karkashin taken " Musulunci da zama dan'kasa…" wanda cibiyar Potugal ta koyar da Larabci da Fulatanci da wayewar Musulunci ta shirya daga ranakun 27 zuwa 28 ga watan Disamba da muke ciki.Taron da ya samu halartar masu bincike da dama ya tattara wasu
26/12/2008
JKMD ta shirya wa matasa 50 taro a Muzambik
A ranar Lahadi 14 Disamba da muke ciki ne, ofishin JKMD dake Muzamabik ya yi bikin kammala taron matasa Musulmi a garin Marombini tare da hadin guiwar kungiyar samari Musulmi ta Muzambik. Taron ya samu halartar matasa kusan 50 samari da ‘yanmata.
Taron ya zo ne cikin jerin ayyukan da JKMD ke yi na kyautata korewar matasa don iya ba da gudummawa a zamantakewa da suke ciki,
26/12/2008
Kungiyar duniya ta zaman lafiya da Kungiyar kasashen Musulmi sun rattaba hannu a JKMD
A ranar Alhamis 25 ga watan Disamba da muke ciki ne, JKMD ta karbi bakuncin rattaba hannu tsakanin Kungiyar duniya ta zaman lafiya da daba da taimakon gaugawa da cibiyarta ke Libiya da kungiyar kasashen Musulmi kan yarjejeniyar fahimtar juna da aiki bai daya,rattaba hannun da aka gudanar a dakin taro na JKMD ya hada da gudanar

Hirar wata-wata

A hirarsa da ya yi da jaridar Al-Dawa a baje kolin Alkur'ani da JKMD ta shirya a Tiripoli, shekh Ahmad Al-Asarawi babban shehin makaranta Alkur'ani a Masar ya jinjina wa Jagoran canji bisa kula da yake ba wa Al-kur'ani mai girma, kuma ya yaba da JKMD bisa hidimar da take yi wa Alkur'ani.
  View this article in PDF format Print article Send article

Banners

Ba mu ra’ayinka

Shin a ganinka internet yana ba da gudunmawa wajen yada da’awar Musulunci?
Kwarai da gaske
Ban sani ba.
Babu shafukan internet na da’awa